ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Malamai da gwamnatin tarayya sun kai karshe

Ministan karatu yace za’a biya bukatun su kuma nan da sati daya ASUU zata dawo garesu bayan sun shawarci sauran yan kungiyar

Bayan zaman da tayi na tsawon sa’o’i 12 da wakilan gwamnatin tarayya kungiyar malaman jami’a ta amince da janye yajin aiki da take.

A rahoton da Premium times ta wallafa shuwagabannin kungiyar malaman jami’a na kasa wanda Biodun Ogunyemi ke jagoranta ta gana da wakilan gwamnatin tarayya wanda ministan ayyuka Chris Ngige tare da Ministan karatu Adamu Adamu suka jagoranta ranar alhamis 7 ga watan Satumba.

Biodun ya bayyana ma yan jarida bayan ganawar cewa ya amince da matsayar da gwamnatin tarayya ta kawo amma zai kai matsayar ga sauran yan kungiyar don suyi nazari a kanshi kana zasu dawo ga gwamnati nan da sati daya.

“Yanzu mun samu matsaya kwakkwara wanda zamu iya kai ma sauran yan kungiya don suyi nazari a kanshi” cewar shugaban kungiyar.

ADVERTISEMENT

A nashi bayanin ministan karatu yace sun shirya biyan bukatun ASUU kuma nan da sati daya kungiyar zata dawo a gare su bayan sun tuntubi sauran yan kungiyar.

Sun fara zaman tun karfe 1:38 na rana har zuwa 2:15 na safe.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT