ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wata kila yan sanda su kama Bukola Saraki

Sufeton yan sanda ya ziyarci fadar shugaban ranar juma'a inda ya bayyana masa wasu takardun shaida kan zargin da rundunar take ma Bukola Saraki domin yazo ya wanke kansa.

Rundunar tana zargin Bukola Saraki da goyon bayan yan fashi da makami da suka kai hari garin Offa dake nan jihar Kwara.

Shugaban kasa ya bayyana cewa bashi da hakkin tare tuhumar da rundunar take yi kan Bukola Saraki yayin da Ibrahim Idris ya kawo masa ziyara a fadar sa.

Bisa ga wannan matakin da shugaban ya bayar, ana sa ran cewa rundunar zata kama Bukola Saraki nan bada dadewadamar.

Shugaban majalisar dattawa ya shiga tarkon yan sanda bayan wasu barayi biyar daga cikin 22 na wadanda suka kai hari garin Offa suka bada amsa cewa shi da gwamnan jihar kwara ke mara masu baya wajen aika aikan da suke yi.

ADVERTISEMENT

Ranar Lahadi 3 ga watan Yuli rundunar ta tura ma jagoran majalisar dattawa takardar gayata domin yazo ya wanke kansa tare da bada amsoshin tambaya kan zargin da ake masa.

Sun bayyana hakan ne bayan da aka garzaya dasu gidan yari dake Abuja daga wanda aka fara tsaran su a kwara.

Sai dai amma Saraki da gwamnan sun nisantar da kansu da wannan zargin inda suka bayyana cewa zargin bata da tushe balle makama.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT