ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tsohon kociyar PSG zai maye gurbin Arsene Wenger

Unai Emery zai koma kungiyar Arsenal bayan doke shekara biyu da horas da tawagar Paris saint germain na Faransa inda yayi nasara lashe kofingasdar Faransa sau daya.

Unai Emery zai koma kungiyar Arsenal bayan doke shekara biyu da horas da tawagar Paris saint germain na Faransa inda yayi nasara lashe kofin gasar Faransa sau daya.

Sabuwar kociyar mai shekaru 46 yayi kaurin suna a kasar andalus sanda ya jagoranci kungiyar Valencia da Savilla. Yayin da yake tare da Savilla yayi nasara lashe kofin zakarun nhiyar turai na Europa league.

Kungiyar Arsenal ta sanar da wannan labarin ta hanyar sakon da shugaban ta, Ivan Gazidis ya fitar ma manema labarai.

Ivan Gazidis ya sanar cewa Arsenal ta zabi Unai Emery bisa kwararsa tare da irin basirar da yake dashi wajen farfado da kananan yan kwallo.

ADVERTISEMENT

Kan matsayin da ya samu, shima sabon kociyar ya mika sakon godiyar sa ga kungiyar bisa damar da ta bashi na jagorantar ta.

A cewar shi, zai yi iya bakin kokarin shi wajen faran ta ran kungiyar da dinbim masoyan ta na fadin duniya.

Unai Emery zai maye gurbin Arsene Wenger wanda ya shafi sama da shekaru 22 yana horas da yan wasan Arsenal.

Wenger ya sanar da yin murabus a karshen kakar bana a wata sanarwa da ya fitar cikin watan Afrilu.

Dan kasar faransa mai shekaru 63, shine kociya mafi dadewa a tamaular firimiya na Ingila kuma yayi nasarar horar da Arsenal a wassanni 823.

ADVERTISEMENT

Yayi murabus ne kafin karewar kwantiragin sa wanda sai cikin kakar badi zai kawo karshe.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT