ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tauraruwar Kannywood ta raba kayan masarufi ga mara hali

Jarumar wanda aka fi sani da Hadiza Gabon tayi hakan ne a garin Kano kuma aiki ne wanda ta saba yi a ko wace shekara.

Bisa wannan kokari da tayi, jarumi wanda aka yi ma lakabi da Sarkin kannywood, Ali Nuhu ya yaba mata tare da wallafa hoton ta sanda take gudanar da rabon kayan masarufin a shafin sa na Instagram.

Tun ba yau ba, jarumar tana daya daga cikin fitattun masana'antar fim dake tallafawa mara sa galihu da arzikin da Allah ya azurta ta dashi.

Tana hakan ne a karkashin gidauniyar ta mai suna Hadiza Aliyu Gabon Foundation.

Hazikar jarumar tana daya daga cikin manyan jarumai da ake damawa dasu a masana'antar fim bisa rawar da take takawa a fim ta hanyar nuna kwarewar ta a ko wani matsayi da aka bata.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT