Shugaban yayi nadin ne ranar alhamis 24 ga watan mayu.
Sunayen jami'o'in gwamnati da shugaban kasa ya nada
Ga sunayen sabbin jami'an da shugaba buhari ya nada tare da hukumar su kamar haka
Ga sunayen sabbin jami'an da ya nada tare da hukumar su kamar haka:
Dokta Anasa Ahmad Sabir - an nada shi a matsayin babban daraktan asibitin koyarwa ta Jami'ar Usman Dan Fodio da ke Sokoto.
Dokta Theresa Obumneme Okoli wadda ya nada a matsayin sabon shugaban kwalejin gwamnatin tarayya dake horas da malamai dake nan garin Umunze na jihar Anambra.
Sai kuma Dokta Emmanuel Ikenyiri wanda ya nada a matsayin shugaban Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake horas da malamai na garin Omoku a jihar Rivers.
Wannan sabbin nade-nade da yayi ya biyo bayan wanda ya yi a farkon watan mayu. Shugaban yayi nade-naden ne a hukumar NDIC da kuma hukumar zabe ta kasa.
Cikin wadanda ya nada a hukumar NDIC akwai babban lauya, Festus Keyamo wanda ya kaddamar a matsayin kakakin yakin neman zaben sa.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng