ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sojoji sun kewaye hedikwatar APC yayin da jiga-jigan jam'iyar ke shirin gabatar da taro

Jiga-jigan jam'iyar APC na kasa baki daya zasu gudanar da taro na musamman a nan ofishin su ranar talata 27 ga watan yau.

Dakarun sojoji da yan sanda sun kewayi babban hedikwatar jam'iyar APC dake nan Abuja domin tabbatar da tsaro yayin da jiga-jigan jam'iyar ke gudanar da taro.

Jiga-jigan jam'iyar na kasa baki daya zasu gudanar da taro na musamman a nan ofishin su ranar talata 27 ga watan yau.

Kamar yadda jaridar  punch ta ruwaito, dakarun cike cikin tireloli dauke da makamai aka baza a garin tare da kafa shingen bincike a hanyar shiga da fita na harabar ofishin.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo tare da sauran gwamnonin jihohi 24 da APC ke shugabanta zasu halarci wannan taron.

ADVERTISEMENT

Ana sa ran cewa jiga-jigan zasu tattauna akan hanyoyi da zasu bi domin samun nasara yayin da zaben 2019 ke gabatowa.

ganawar da shugaba Buhari yayi da wasu jiga-jigan jam'iyar mai ci a fadar shi nan Villa, shugaban ya shawarce su da su fara shirya ma zaben dake gabatowa.

Duk da cewa har ga yanzu shugaban bai sanar cewa zai fito takara, ana kyautata zaton cewa zai bayyanar da hakan nan ba da jimawa.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT