A wata takardar sanarwa da kakakin rundunar sojojin na kasa Birgediya janar Texas Chukwu, kakakin yace an kama wasu mabarnatan su shida yayin da suke cikin aikata laifin a yankin kwata suke kuma mutum biyu sun tsere yayin da dakaru ke sintiri a gundumomin Chembe, Tse-Gundu, Tse-Iordye da Sbaor na jihar.
Sojoji sun kama wasu makiyaya 18
Kakakin ya bayyana cewa an mika wadanda aka kama ga hukumar yan sanda domin cigaban bincike kafin a gurfanar dasu gaban kotu domin zantar da hukunci
Makiyayan sun tsere daga kamuwa kana sun bar baburar su an kuma gano bindiga yayin yayin da sojojin ke safara.
Kakakin ya bayyana cewa an mika wadanda aka kama ga hukumar yan sanda domin cigaban bincike kafin a gurfanar dasu gaban kotu domin zantar da hukunci.
Birgediya Chukwu ya kuma sanar cewa an kama wasu makiyaya su 12 a gundumar Mbayer/Yandez da Kaambee na jihar yayin da suke aiwatar da barna a gonakin jama'a.
Rikicin jihar Benuwe
Jihar Benuwe ta sha fama da rikicin makiyaya da manoma wanda sakamakon rikicin an rasa rayukaa tare da salwantar dukiyoyi.
A ranar 5 ga wata mutum 24 sun rasa rayuka sakamakon harin da wasu da ake zargin cewa makiyaya ne suka kai garin Omusu Edimoga na karamar hukumar Okpokwu.
Lamarin ya biyo bayan binne mutum 73 da ri gwamnatin jihar tayi wadanda suka rasa rayukan su sakamakon rikicin da ya barke cikin 11 ga watan janairu na 2018.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng