ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Zan fito takara a zaben idan PDP ta amince da fitowa ta - inji tsohon gwamnan Jigawa

Lamido yace yana sa ran fitowar mutane da dama domin neman kuri'a a zaben 2019 karkashin jam'iyar PDP

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido yace zai fito takarar shugaban ƙasa a zaben 2019 idan jam'iyar PDP ta amince da fitowar shi.

Lamido yayi wannan sanarwan a wata wasika ya tura ma wasu membobin jam'iyar sa ranar 22 ga watan octoba.

a cikin wasikar tsohon gwamnan yace ya zama dole jam'iyar adawa ta PDP ta dawo da shugabancin ƙasar domin tarban yan ƙasa zuwa hakikanin tudun tsira da suke nema.

Yayi iƙirarin cewa shekara 57 kenan da samun yanci amma har yanzu ba'a cinma burin iyayen kasa da suka taimaka wajen kwato yancin.

ADVERTISEMENT

Da wannan yake gabatar da kanshi ga jam'iyar cewa yana da niyar fitowa takara amma sai dai idan ta amince da fitowar shi.

Lamido yace yana sa ran fitowar mutane da dama domin neman kuri'a a zaben 2019 karkashin jam'iyar PDP.

Ya kara da cewa ya san cewa ba shi kadai bana wanda yafi cancanta amma yana kira da babban murya kuma yana adu'a na a tabbatar da an zabi wanda zai jagoranci jam'iyar a zaben 2019 cikin adalci kuma a zabi wanda yafi cancanta.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT