ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Buhari ya ƙaddamar da kamfanin sarrafa abincin kaji a jihar Kaduna

Shugaban yayi tafiya zuwa Jihar don ƙaddamar da katafaren kamfanin sarrafa abincin kaji da sauran dabbobi

Yau 12 ga watan Satumba shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi jihar Kaduna don ƙaddamar da kamfanin Olam.

Kakakin shugaban ƙasar Bashir Ahmad ya sanar da aka a shafin sa na twitter tare da hotunan isowar shugaban.

Gwamnan jihar Kaduna mallam Nasir el-rufai ya tarbi shugaban yayin da ya iso wurin kaddamar da kamfanin

Kamfanin wanda aka gina a karamar hukumar Chikun da $150M (kimanin naira biliyan 20) zata samar ma matasa 8000 aiki tare da likitocin dabbobi 200.

ADVERTISEMENT

“Don amfanin al’ummar jihar Kaduna da ma ‘yan Nigeria baki  daya na kaddamar da wannan kamfanin da yardar Allah” sakon shugaban yayin da yake bude kamfanin.

Manyan baki da suka halarci wajen bikin bude kamfanin sun hada da mai martaba sarkin kano Alhaji MuhammadSanusi (na biyu) , ministan noma Audu Ogbeh, gwamnan jihar KebbiAlhaji Atiku Abubakar Bagudu, gwamna Nasir El-rufai da mataimakin sa Bala Bantex.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT