ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Buhari tare da wasu jiga-jigan gwamnati sunyi addu’o'i ta musamman ma ƙasa

Shugaban tare da wasu ma’aikatan gwamnati sunyi ma kasa addu'o'i yayin da suka halarci sallar juma’a a masallacin dake fadar shugaban ƙasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da wasu manyan yn kasar sun halarci sallar juma’a a massalacin fadar shugaban kasa na Aso villa ranar juma’a 29 ga watan Satumba inda suka yi ma kasar addua yayin da ranar bikin cika shekara 57 da samun yancin kai ke gabatowa.

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki tare da gwamnan jihar Bauchi Abubakar Muhammad da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo da wasu ministocin ƙasar sun hadu da shugaban wajen yin addu’o’in.

Kakakin shugaban Bashir Ahmad ya sanar da haka a shafin sa na twitter inda ya sanya bidiyo wanda ke nuna shugaba yayin da yake gaisawa da baƙin sa bayan sun kammala sallar.

ADVERTISEMENT

Sauran jiga-jigan gwamnati da suka halarci masallacin sun hada da shugaban rundunar sojojin kasa Lt.Gen Tukur Buratai tare da Shugaban rundunar sojojin sama Air marshal Sadique Abubakar har da Sifeton yan sanda Ibrahim Idris.

Nijeriya zata yi bikin cika shekara 57 da samun yancin kai daga mulkin mallakar turawah ranar lahadi 1 ga watan octoba 2017.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

Top 5 female directors in Nollywood

Top 5 female directors in Nollywood

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 reasons Easter was more fun when we were children

5 reasons Easter was more fun when we were children

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT