ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari yayi jimamin mutuwar tsohon ministan Nijeriya

Alhaji Hassan Lawal ya rasu ne safiyar ranar lahadi 25 ga watan Maris a wata asibiti dake Abuja bayan wata rashin lafiya da yayi.

Alhaji Hasan Lawal ya rasu ne safiyar ranar lahadi 25 ga watan Maris a wata asibiti dake Abuja bayan wata rashin lafiya da yayi.

A sakon jaje da mataimakin shugaban kan harkar watsa labarai Shehu Garba ya fitar ma manema labarai, shugaban ya jajanta ma iyalen sa da al'ummar jihar Nasarawa bisa babban rashi na suka samu.

Shugaban ya yaba halayen tsohon ministan inda ya kwatanta shi a matsayin ginshiki wanda ya taka rawar gane a siyasar jihar Nasarawa da ma yankin arewa ta tsakiya.

Yayi ma sa addua na Allah ya rahamshe shi kana ya jajanta ma iyalen sa da gwamnatin jihar Nasarawa.

ADVERTISEMENT

Shugaban ya tura tawagar fadar sa zuwa jihar Nasarawa domin yi ma iyalen marigayi ta'aziya.

Tawagar gwamnatin tarayya ya hada da ministan muhalli Malam Ibrahim Jibril da kuma Shehu Garba da Abba Sarki da shugaban hada-hada na fadar shugaban Ambasada Lawal Kazaure.

Gwamnan jihar Nasarawa Umar Tanko Al-makura da sarkin Keffi mai martaba Dakta Shehu Chindo Yamusa sun yi ma shugaban godiya kan matakin taya jihar da iyayen marigayin bakin ciki rashin da suka samu.

Anyi jana'izar marigayin a Keffi garin mahaifar sa.

Alhaji Hassan Lawal ya rike mukamin ministan muhalli da kuma ministan kwadago da ministan kiwon lafiya a karkashin mulkin tsofin shugabannin kasa Umaru Musa Yar'adua da Goodluck Jonathan.

ADVERTISEMENT

Marigayij ya rasu yana da shekaru 64 a duniya kuma ya rasu ya bar matansa biyu da yara shida.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT