ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari yayi ganawan sirri da tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo

Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasan bai bayyana batun da suka tattauna a kai da shugaban ba yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai

Kamar yadda rahotanni suka zo mana, ganawan nasu bai kai kimanin sa'a daya ba.

Sai dai shi tsohon mataimakin shugaban kasa bai kara haske kan abubuwan da suka tattauna akai shugaban ba yayin da manema labarai suka tunkare shi bayan kammala ganawar.

Idan ba'a manta ba a ranar 2 ga watan febreru hukumar dake hana cin hanci da rashawa ta EFCC ta far ma wata dukiyar Namadi Sambo dake nan Abuja.

Jami'an hukumar sun ziyarci dukiyar domin yin bincike kan zargin da ake masa kan taqaddamar almumdahana na Dasuki wanda ake tuhuma har yanzu.

ADVERTISEMENT

Sambo shine mataimakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan daga watan Mayu na 2010 zuwa 2015 a karkashin jam'iyar PDP.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT