Babban malamin ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi 6 ga watan Mayu, a gidan sa dake nan unguwar Liman na garin Katsina. Anyi jana'izar shi karfe 2:30 na rana.
Shugaba Buhari ya taya jihar sa jimamin mutuwar babban limami
Babban malamin ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi 6 ga watan Mayu, a gidan sa dake nan unguwar Liman na garin Katsina. Anyi jana'izar shi karfe 2:30 na rana
A wata takardar sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu ya sa hannu, shugaban ya taya iyalan marigayi da sauran al'ummar jihar juyayin mutuwar sa.
Kamar yadda takardar ta bayyanar, Shugaban ya yaba halayen marigayin bisa yadda ya tafiyar da rayuwar sa wajen raya addinin musulunci.
yayi kira ga jama'a da a yi koyi da kyakkywar halin sa na zama tare da mutane cikin soyayya da zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa da makwabta da sauran jama'a.
Daga shugaban, ya yi ma marigayin addu'ar Allah ya jikan shi da rahama tare da yi iyalen sa addu'ar Allah ya basu hakurin jure rashin sa.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng