ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaban ƙasa ya koma Abuja

Buhari ya yaba ma sarkin Daura bisa karamci da ya nuna

Shugaban ƙasa Buhari ya bar Daura ya koma Abuja bayan kammala hutun babban sallah da yayi a mahaifarsa.

Rahoto daga kamfanin dillancin labarai (NAN) ya nuna cewa shugaban kasa ya bar Daura karfe 10:24 na safe a jirgin mai saukar angulu na fadar shugaban ƙasa.

Cikin tawagar sa akwai iyalinsa, hadimin sa Garba Shehu, babban jami’in tsaro na shugaban Bashir bindawa da sauran fadawan sa.

Shugaban ya yaba ma sarkin Daura Alhaji Umar Faruq bisa karamci da ya nuna ma takwaransa shugaban kasar jamhuriyar Nijar Mahamadou  Yusouffou lokacin da ya ziyarci fadar sarkin ranar talata.

ADVERTISEMENT

Sarkin daura da manyan yan siyasa tare har masu yi mai fatan alheri suka taka ma shugaban baya har inda ya hau jirgi.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT