ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sanata yace minista tayi Murabus

Wannan ya fito bayan ta goyi bayan tsohon mataimakin shugaban a kan zaben 2019

Sanata Shehu Sani ya shawarci  ministar harkokin mata Aisha Alhassan akan tayi murabus.

Wannan ya fito bayan ministan ta nuna cewa zata goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasa a zaben 2019.

A bisa rahoton da Daily post ta fitar, sanatan ya gargadi Aisha da ta bar majalisar Buhari indai ta san zata goya ma Atiku baya a zaben 2019.

Sanatan mai wakiltar jihar Kaduna yana cewa “ babbancin wannan matar da tayi wannan magana da sauran mutane shine ita ta fito fili ta bayyana abun dake ran ta yayin da sauran suna boye abubuwan dake nasu zuciyar”.

ADVERTISEMENT

“Indai ta shirya aiki da tsohon mataimakin shugaban kasa, toh tana iya fita daga wannan gwamnati kuma taa maida hankali akan abun dake ranta”.

Ministan dai tace bata tsoro na a kore ta daga aiki don maganar da tayi.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT