ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

shahararen mawaki ya zama ango

Biki n wadda aka yi a garin jos ranar asabar wanda ya samu halarcin wasu manyan yan wasan kwaikwayo na masana'antar kannywood

Garin jos ya karbi bakoncin manyan jarumai daga masana'antar kannywood yayin da aka daura auren shaharraren mawakin garjiya na hausa Saed Yahaya Abubakar wanda aka fi sani da Saed Nagudu.

Anyi daurin auren ranar juma'a 15 ga watan Satumba a layin Dan karfalla dake garin Jos na jihar Filato.

Auren saed nagudu da Khadija Ahmad Yusuf an kwashi kwana uku ana shagulgular bikin inda aka shirya bukukuwa kamar kamu, wassan kwallon kafa, Artist day,Arabian night da sauran su.

ADVERTISEMENT

cikin wadanda suka halarci bikin akwai shahararen jaruman fina-finan hausa Sadiq Sani Sadiq, Saleem Ahmed Saleem da Muhammed Bello wanda aka fi sani da 'general bmb'.

Sauran yan wasan kwaikwayo da mawakan hausa sun nuna murnar su game da auren inda suka daura hotunan angon da amaryan shi a shufukar su na kafar sada zumunta tare da yi masa fatan alheri.

Daga gare mu nan a sashen hausa na Pulse muna ma ma'auratan fatan Allah ya bada zaman lafiya.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT