ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan majalisar dattawa zai amsa tambayoyi game da zargin da yayi ma sufeton yan sanda na kasa

Misau yayi ma Sufeton yan sanda Ibrahim Idris zargin amsar cin hanci daga kamfanoni da dama inda yake tura jami'an tsaro

Sanata Isa Misau zai gabatar da kansa gaban kwamitin bincike na majalisar dokoki yau ranar litinin 23 ga wata bisa ga zargin da yayi ma babban sufeton yan sanda na ƙasa Sufeto janar Ibrahim Idris.

Shugaban kwamitin kuma mataimakin shugaban jam'iya mafi rinjaye na majalisar Francis Alimikhena ya sanar da haka ranar lahadi a garin Abuja.

Misau yayi ma Sufeton yan sanda Ibrahim Idris zargin amsar cin hanci daga kamfanoni da dama inda yake tura jami'an tsaro.

Ya kara da cewa sufeton yana amsar makudan kudade daga jami'an da ya daga matsayin su a hukumar a matsayin cin hancin daukakan da yayi masu.

ADVERTISEMENT

Sanatan ya kara da cewa Sufeton yayi ma wasu jami'an hukumar ciki kuma ya daukaka martabar su wanda yin haka ya saba ma kundin tsarin hukumar.

Idris Ibrahim ya musanta wannan zargin har ma gwamnatin tarayya ta daukaka karar zargin da Misau yayi zuwa kotu.

A matsayin shi na tsohon jami'in hukumar suma hukumar yan sanda sun mayar masa da martanin a baya inda suke zargin shi da barin aiki ba tare da anyi masa bikin domin kaurace wata horo da za'a gudanar a kan sa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT