ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Madrid ta gamu da dodonta a Santiago bernabeu

Duk da dawowar Cristiano Ronaldo wannan bai hana Antonio Sanabria daukaka tawagar shi inda ya sa kwallo a ragar Navas gab da za’a tada wasan

Zakarun turai Real madrid sun ji ba dadi a hannun Real betis wasan su a filin santiago bernabeu ranar laraba 20 ga watan Satumba cikin gasar gane zakarun Spain na La-liga.

Wannan shine karo na farko da Madrid zata rasa maki daga hannun Real Betis tun 1998 kuma shine wasa cikin wasanni 74 da Madrid bata sa ƙwallo ko daya a raga.

Cikin minti 93 na wasan Antonio Sanabria na Betis yasa ƙwallo a ragar Madrid.

Duk da dawowar Cristiano Ronaldo wannan bai hana Sanabria daukaka tawagar shi inda ya sa ƙwallo a ragar Keylo Navas gab da za’a kammala wasan.

ADVERTISEMENT

Ronaldo wanda ya samu dakatarwa na wasanni 5 bai samu damar nuna ma Betis dalilin da yasa aka laƙa mai “zakaran turai” inda tsohon mai tsaran gidan Madrid Antonio Adan wanda ya sauya zuwa ga Betis ya hana shi nuna ƙwarewarsa.

Sandiyar wasan da suka rasa maki yanzu Real madrid tana bayan Barcelona da maki 7.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT