ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Jarumi ya bayyana dalilin da yasa duk 'yan gidan su ke fitowa a fim

Ya kara bayyana dalilin da yasa yayi soyyaya da kanwar sa Maryam a cikin wani sabon fim mai suna Gwarzon shekara

Shaharren dan fim kuma fitaccen furodusa ta masana'antar Kannywood Ramadan Booth ya bayyana dalilin da ya sanya duk yan gidan su ke yin fim.

Daga uwar su  Zainab Booth zuwa Ramadan Booth da Maryam Booth da Amude Booth wannan iyalin sun dade suna nishadantar da yan arewa.

A hirar sa da BBC hausa, Ramadan ya bayyana cewa dalilin da yasa yan gidan su ke fiitowa a fina-finan hausa shine don kawar da zargin da ake wa yan fim na cewa yan fim na bata tarbiya.

Jarumi wanda ya ziyarci birnin London inda ya amshi kyautar gwarzon shekara wanda Mujallar African Voice ta shirya ya shaidawa BBC cewa suna fitowa a fim don kawar da zargin.

ADVERTISEMENT

Ya bayyana dalilin da yasa yayi soyyaya da kanwar sa Maryam a cikin wani sabon fim mai suna Gwarzon shekara.

"ban dauki hakan a matsayin wani abu ba. Babu abin da na ji yayin da na fito a fim, ina soyayya tare da kanwata Maryam. Kuma na yi amfani ne da abin da darakta ya ba ni umarni na yi." Dan wasan ya shaida wa BBC hausa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT