ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kamfanin ClassiQ sun nemí gáfara wajen ʼƳar Wasar Ƙwaikwaiƴo

A cikin kwanan nan, an dakatar da Rahama Sadau daga Kannywood domin fitaʼn da ta yi a wani waƙa na ClassiQ, mai zama a gari’n Jos.

Kamfanin ClassiQ sun nemí gáfara wajen ʼƳar Wasar Ƙwaikwaiƴo

ClassiQ ya bada hakuri domin wannan dákátárwa wanda aka yi ma Rahama daga Ƙungiyar Masu Wasaʼn Ƙwaikwaiƴo na Arewa.

An buga akan wani bayani na Ƙungiya masu hoto da wasaʼn Ƙwaikwaiƴo na Najeriya cewâ a kan dakatar da Rahama domin wasa wanda ta yi tare da Ma-waƙa mai suna ClassiQ. ClassiQ ya bada haƙuri akan Instagram domin wannan faruwá. Ya rubuta wasiƙa kamar haka:" Bayan mun gama sakin waƙar vidiyo na ʼI love youʼ wanda Avala ya yi tare da mu (Rahama da ni ClassiQ), na samu labari na zargi wanda wasu sun yi ma Rahama.

Ko da yake ina da raʼayi na harkaʼn waƙa, rawa, da kuma Ƙwaikwaiƴo, ina hankali wajen kula da matsala na bambanci na alʼaduʼn mu, wanda muke fuskanta da shi. Domin haka, báyáʼn haƙuri da na ba Rahama cikin saƙo wanda ná rubuta zuwà gare ta, na fita ga hili gaban kowa in ƙara ba da haƙuri domin matsaloli da sakamako na halin da áke cikí.

ADVERTISEMENT

Ina son in roƙi maʼaboci da jamaʼa gaba ɗaya masu kaunaʼn waƙoki na, su yi haƙuri. Duk wandá mun ɓata ma rai, muna neman gafará wajen kû.  Rahama, Allah ya albarkacé ki da bàsiraâ, da kuma fasaha na iya wasa, da koƙarfi. Saboda haka, ke zama abin kwatanci ga duk masu neman ƙwarewa ga harkaʼn wasaʼn Ƙwaikwaiƴo. Nagode da ké yardá da kamunʼ hannû da wannan wasa.”

Daga ni, ClassiQ.

Sakatare na  Ƙungiyar masu hotó da wasaʼn Ƙwaikwaiƴo na Najeriya-mai suna Salisu Muhammad- ya bada bayani akan Dakatarwa wandán aka yi wa Rahama Sadau a cikin takaddar ƙungiyar wanda shugabanci na ƙungiya sun sa hannuʼn su ga takkada.

A ranar huɗu ga watar Oktober, Rahama ta rubuta wasiƙa game da wannan matsala, kuma ta roƙi gafará ga waddanda abin ya shafá. Rahama ta na shirin fita a wani sabon vidiyo na Nollywood mai suna Ajuwaya da kuma wani vidiyo mai suna “Hakkunde”, da kuma wani dogon shiri "Sons of the Caliphate" waton ʼƳan Khalifa" na Kamfaniʼn Ƙwaikwaiƴo mai suna EbonyLife TV.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT