ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mun yarda kasar mu ta kasance akwai hadin kai’. Inji mukaddashin shugaban kasa

Mukaddashin shugaban kasa yayi wa’azin hadin kai a kasar a wanan lokacin da yan arewa da yan kudu maso gabas ke neman farkewa

Prof Yemi Osinbajo

Jiya 19 ga watan yuni, mukaddashin shugaban kasa ya gana da sarakunan arewa a tsohon fadar shugaban kasa.

Ganawar yana daga cikin hanyar neman sulhu wadda Osinbajo keyi dangane da wa’adin da ƙungiyar matasan arewa suka bada na cewa yan kabilar ibo su bar yankin.

Yayi jawabi na samun hadin kai a duk fadin kasar don maganta il’lar da wa’adin ke nemar haifarwa tun daga ranar da aka bada wa’adin.

“Bari in sanar maku cewa ina mai farin ciki da girmamawa da wannan ziyarar da masu martaba suka kawo min.

ADVERTISEMENT

Duk da cewa yau da safe Sultan ya dawo daga kasar waje ya samu damar halarci wannan gurin.

:

“Ina godiya da zuwan ka wannan taron iftar har ma zaka jira zuwa gobe duk da cewa kana da abubuwa daka tsara.

“Kasar mu na bukatar shugabanci kamar yadda ka nuna kuma ina godiya da shugabancin da ka nuna”

“Abun farin ciki ne ganin shugabanin mussaman sarakuna sun shirya bada jinin su don ganin kasar mu ta zauna lafiya. Ina maku godiya”

ADVERTISEMENT

“Mussamman inama Sultan godiya da ya kasance a ko wani lokaci a shirye yake ya bada shawara ko ya bada wata hanyar saukar da wata matsala, ina mai matukar godiya dangane da duk goyon baya da kake bani’.

“Yadda muke ganin abubuwa na tasowa a cikin al’ummar mu a yau (har da na cikin gida) ba abun farin ciki bane.’

“Duk mun yarda cewa dole kasar mu ta zauna cikin hadin kai. Da muka yi magana da shugabanin kudu maso gabas duk da hada-hadan da ya faru na fahimci cewa dole kasar mu ta zauna cikin hadin ka”

“Kamar yadda na gayama shugabanin yankin kudu maso gabas, an rasa rayuka da dama wajen ganin cewa an zauna lafiya, amincin mu ga waddanda suka sadaukar da rayukan su dan samun haka shine mu tabbatar cewa mun cigaba da zaman lafiya da hadin kai’

“Kasar mu na da albarka kuma muna da damar ganin cewa mutanen mu sun san albarkan dake cikin ta’

ADVERTISEMENT

“Bayan haka ina maku godiya da wannan alherin da kuka yi min na halartar wannan iftar

“Ina addua Allah ya sanya albarka a masarautar ku, ya kuma baku sahon rai na mulki cikin lamin-lafiya.

“Nagode” yace.

A wata bayani da ƙungiyar matasan arewa suka bada a ranar 6 ga watan yuni, sun dau alkawarin aiwatar da duk wani aiki na ganin cewa wa’adin da suka ba yan kabilar igbo na barin yankin kafin 1 ga watan octoba ya zauna.

Wannan bayani ya sa gwamnan kaduna Nasir El-rufai ya bada umurni da a kama yan ƙungiyar.

ADVERTISEMENT

Bayan ganawar da Osinbajo yayi da shugabanin siyasa da na addini na yankin arewa, ya bada gargadi cewa duk wanda ke da hannu wajen bada wannan wa’adin yana gab da ƙurkuku don sun saɓa wa dokar kasa

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT