ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mukaddashin shugaban kasa yayi kira ga sarakunan arewa da su tashi tsaye wajen hana kalamin tunzura

Osinbajo yace ganawar ya zama wajibi a gareshi don magance maganganun raba kasa da ke yaduwa a kasar tun makonin baya.

Professor Yemi Osinbajo

Ranar talata da ta gabata mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya gana da sarakunan arewa inda yake kiran su da su tashi tsaye wajen hana kalamin tunzura a masarautar su.

Yayin gabatar da ganawar da aka yi a babban zauren fadar shugaban kasa, mukaddashin yace; ganawar ya zama dole a gareshi don magance maganar raba kasa da ke yaɗuwa tsanin yan kudu maso yamma da yan Arewa.

“Ina sane da gudumawar da kuka bada a baya wajen neman cigaban kasar. Matsayin ku cikin kasa nada matukar amfanin don magance il’loli dake damun kasar mu”

“Dalilin ganawar da nake ta yi hakika a fili yake,; don magance illar da maganganun dake yaɗuwa tun watanni baya wadda ke neman hadasa ga’ba tsakanin yan kudu maso yamma da yan arewa”

ADVERTISEMENT

“Muna sane da wa’adin da wasu kungiyoyin matasan arewa suka bada na cewa yan kabilar igbo su bar yankin arewa”

“Kafin wannan akwai kuka wadda har yanzu ke bazuwa inda wasu kungiyoyin matasan yankin kudu maso yamma karkashin jagorancin IPOB inda suke nema a raba su da kasar  naijeriya”

“A duk ganawar da mukayi da shugabanin yankin kudu da arewa, mun dauki mataki daya wadda itace kasar mu zata samu nasara idan muka zauna lafiya da hadin kai. Ina mai jaddadawa cewa baza mu yarda da maganganun tunzura dake yaduwa don bai da tushe a tsarin dokar kasa”  yace.

Mukaddashin shugaban kasa ya bayyana ma sarakunan cewa akwai rawan da zasu taka wajen hana kalamin tunzura dake yaduwa a kasar.

Ya kara da cewa kasar ta riga ta gan illar da irin wannan maganganun ke haifarwa inda yace jinin  sojoji da mutane da suka rasa rayukansu a baya ya riga ya biya farashin zaman lafiya.

ADVERTISEMENT

Ya rufe da yi ma sarakunan godiya har ma ya kara da yi masu addua cewa Allah ya kara masu basira da tsahun rai na mulkan masarautar su cikin koshin lafiya.

Ganawar ya samu halarcin manyan mutane da dama irin su, sarkin musulmi Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III; sarkin Kano Muhammad Sanusi; Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar; Alhaji Muhammed Isah Muhammed sarkin jama’a dake kaduna; sarkin garin gummi Justice Lawal Hassan; wakilin sarkin katsina, Prof. Sani Lugga, jagoran majalissar sarakuna, Sakaruyi na Karo, Dr. Emmanuel Kyauta;  Alhaji Ibrahim Gambari, sarkin Illorin; sarkin garin lafiya dake jihar Nasarawa, Alhaji Mustapha Agwai II; shehun bama Alhaji Kyari Umar El-Kanemi, wanda ya wakilci shehun borno; Gbong Gwon Jos, Jacob Buba Jang; sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar; ; Ndakwo Ameh Oboni II, Attah Igala na jihar kogi; sarkin fika na jihar Yobe, Alhaji Muhammadu Ibn Abali; sarkin garin anka dake jihar zamfara Alhaji Attahiru Ahmed Muhammed; Prof. James Ayatse, Tor Tiv na jihar Benue; sarkin garin Abaji Alhaji Adamu Baba Yinusa;  shugaban ma’aikata na shugaban kasa  Abba Kyari; ministan kimiyya da fasaha, Ogbonaya Onu; ministan aikin gida,  Abdulrahman Danbazzau; mai ba kasa shawara kan tsaro, Babagana Munguno, harda kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

Top 5 female directors in Nollywood

Top 5 female directors in Nollywood

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 reasons Easter was more fun when we were children

5 reasons Easter was more fun when we were children

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT