ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Barawo mai damfara maza bisa ga shigar mata ya shiga hannu

An kama shi sanye da hijabi da kwalliya a fuska tare da takalman mata da jakar hannu irin ta mata

Kamar yadda yan sanda suka bayyana, matashin ya bada amsa cewa yana karbar kudi ta barauniyar hanya daga maza bisa ga yadda yake bayyana kansa a matsayin budurwa mai neman saurayi.

An kama shi sanye da hijabi da kwalliya a fuska tare da takalman mata da jakar hannu irin ta mata.

Dan asalin garin Maitumbi dake nan Minna, Abubakar ya shaida cewa watanni da dama kenan yake yin wannan  mummunar sana'ar kuma yayi nasara wajen karban kudi da maza da dama.

ADVERTISEMENT

Ya kuma bayyana ya zabi yin haka ne bayan da sana'ar shi na siyar da sabulu bata kawo masa jari ba bayan watanni da dama da yin sana'ar.

Sai dai mazajen da yake yaudarar basu taba yin nasarar wajen samun bukatar da suke nema daga dareshi domin yakan saba alkawarin da suke yi bayan ya amshi kudi a hannun su da tunanin zasu hadu a wani guri kebatacce.

Ya shaida cewa yafi gudanar da ayyukan shi ga fili a dai dai akwai jama'a domin gudu ma tonon asiri.

Daga karshe yayi mamakin yadda mazajen suke bibiyan shi a mai akon ainihin yan matan dake garin Minna. Yace dai yayi hakan ne bisa ga yanayin rashin abinci da yamayin rashin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT