ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Muna kyautata zato Buhari zai kubutar da yaran mu - inji iyayen matan da aka sace

Iyayen sun amince da alkawuran da shugaban ya dauka na kubutar da yaran nasu

Iyayen yan matan makarantar Dapchi da boko harama ta sace sun ce suja kyautata zato shugaban kasa Muhammadu Buhari zaiyi nasara kubutar da yaran su.

Wannan ya biyo bayan ziyarar jinkai da shugaban ya kai masu ranar laraba 14 ga wata.

Shugaban kungiyar iyayen Malam Bashir Manzo ya bayyana ma manema labarai cewa ziyarar da shugaban ya kawo masu ya rage bakin cikin su kuma ya tabbatar masu da samun nasara wajen dawo da yaran

"Mun saurari abubuwan da shugaba Buhari ya fada. Munyi imani kuma muna kyautata zato kan abubuwa da ya fada. ya karfafa gwiwar mu wajen ganin an kubitar da yaran mu" yace.

ADVERTISEMENT

Ya kuma kara da cewa zasu dukufa wajen bin shawarar da shugaban ya basu na yin addua.

Wata mahaifiyar daya daga cikin yan matan mai suna Maimuna Usman tana mai cewa:

"Shuagaba Buhari mutum ne mai cika alkawari, ba ma shakkun kalaman da yayi na cewa sun tsawaita matakin kubutar da yaran.

"Na aminta da shugaban, ziyarar da ya kawo mana ya huce mana bakin cikin da muke kuma muna sa ran zai dawo da yaran mu.

Shima Muhammed Ali ya kara inda ya bada misalin nasarar da gwamnatin buhari tayi na kubutar da wasu daga cikin yan matan chibok da aka sace a ,mulkin gwamnatin kafin nasa. Ya kuma yi la'akari da malaman jami'ar Maiduguri da mata 10 da aka saka kwanan baya.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT