ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Har yanzu bamu gama yakar Boko haram ba amma muna dab da samun nasara a kan su - inji fadar shugaban kasa

Femi Adeshina yana mai cewa har yanzu ba'a gama yakar boko haram ba amma an rage karfin su kuma nan bada jimawa ba za'a samu nasara a kan su

Yace duk da cewa har yanzu ba'a gama gwaggwarmaya da yan ta'addar ba amma ana dap da samun hakan.

"indai mai yakar su gaba dayan su toh lalle bamu samu nasara ba amma maganar rage karfin su, lalle mun  ci nasara a wannan bangaren"Yace.

kakakin ya bayyana hakan yayin da ya zanta da gidan telibijin na channels a cikin shirin tattaunawa a kan harkar siyasa ranar 25 ga wata.

Duk da hare-hare da yan boko haram suka kai wanda keyi ma harkar tsaro barazana tare da sabon farmaki da suka kai garin Dapchi wanda suka yi awon gaba da yan matan makaranta su 105, kakakin yace gwamnatin shugaba Buhari ta samu cigaba wajen yakar ta'adanci a kasar fiye da yanda suke a gwamnatocin da.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT