ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Matasa sun nuna fushin su ga dan majalisa mai wakiltar su tare da kona gidan sa

Rikici ya barke tsakanin matasa da dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar kwara kuma tsohon gwamnan jihar yayin da matasan suka hana shi shigowa garin sa.

Hukumar kare lafiya jama'a ta tabbatar da mutuwar mutum sanadiyar harbin bindiga da aka yi a garin Lafiagi na karamar hukumar Edu dake nan jihar Kwara.

Kakakin hukumar mista Kunle Bilesanmi ya sanar ma manema labarai cewa wasu mutanew sun kone gidan wani dan majalisar dattawa Sanata Muhammed Sha'aba (mai wakiltar jihar Kwara). Kakakin dai yace hukumar bata da tabbacin mutanen da aka kashe sanadiyar harbin bindiga da aka yi.

Labari ya nuna cewa rikici ya barke tsakanin matasa da dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar kwara kuma tsohon gwamnan jihar yayin da matasan suka hana shi shigowa garin sa.

Majiya sunce matasan sun hana shi shigowa garin bisa ga bukatar da suka kai masa na gyaran wani titin hanyar gari wanda shi dan majalisar yaki gyarawa.

ADVERTISEMENT

A hanyar sa shigowa garin domin gabatar da zabe na mazabar shi matasan suka hana shi shigowa inda suka kudurce cewa sai ya bi hanyar da suka bukace shi da ya gyara bayan ya biyo wata hanya daban.

Ganin yadda matasan suka jajirce da rigimar da suka kawo shine sanatan ya nemi taimako daga jami'an tsaron sa da su taimaka wajen kawar da matasan daga hanyar.

Jim kadan bayan isowar su jami'an suka yi harbi ga iska domin razanar da matasan amma harbin da suka yi ya kai ga wasu daga cikin matasan har ma yayi sanadiyar kashe mutum uku.

Majiya sunce sakamakon aikin da jami'an tsaron suka aikata ya sanya matasan suka kone gidan dan majalisar.

Wani daga cikin yan garin wanda dan uwansa na cikin wadanda aka kashe yayi barazanar hana gudanar da zabe a garin.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT