ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ministan Buhari ya fallasa albashin da suke samu ko wani wata

Ministan ya bayyana cewa ko wani minista na samun N950,000 ko wani wata a matsayin albashi

Ministan sufurri kuma tsohon gwamnan jihar Ribas Rotimi Ameachi, ya bayyana cewa suna samun N950,000 ko wani wata a matsayin albashi.

Ministan ya bayyana  hakan ne a Abuja a taron kaddamar da sabuwar littafi da tsohon ministan ayyukan waje marigayi Mathew Mbu ya rubuta.

Ameachi  yace a cikin albashin ministocin ke cire kaso na jami'o'i dake aiki karkashin su.

"Ko wani minista na amsar albashin N950,000 ko wani wata. N350,000 daga cikin kudi na muhalli ne kuma sauran N600,000 da ya rage ciki za'a biya hadimai da sauran ma'aikata dake aiki karkashin ministan." yace.

ADVERTISEMENT

Ministan ya kara da cewa gwamnatin shugaba Buhari ta takaita yawan badakala da jami'an gwamnati keyi da kudi.

A cewar shi an samu raguwar barnar kudi da yawan hada bukukuwa mara amfani da jami'o'in gwamnati keyi a da kasancewar rashin bude kofar badala da gwamantin yanzu ta kafa.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT