ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Matan arewa 5 da suka kafa tarihi a Nijeriya (hotuna)

Don taya iyayen mu mata raya wannan gangarumar ranar ga wasu matan arewa 5 da suka kafa tarihi bisa mukamin da suka samu sakamakon gwagwarmayar da suke

Ranar 8 ga watan maris na ko wace shekara majalisar dinkin duniya ta ware ta a matsayin ranar mata domin bikin nuna cigaban da mata suka kawo a duniya.

Bisa wannan dalilin muka kawo maku wasu matan arewacin Nijeriya fara kafa tarihi ta hanyar zamowa mata na farko da suka rike wani mukami. Ga su kamar haka:

1. Naja’atu Bala Mohammad

Naja’atu Bala Mohammad ce mace ta farko da ta zama shugabar kungiyar daliban jami’a a Najeriya. An haife ta a garin Kano a shekarar 1966. Ta zama shugabar dalibai lokacin tana karatu a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

ADVERTISEMENT

2. Amina Muhammed

Amina  Muhammed ce mace ta farko 'yar Najeriya da ta zama mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya. 'Yar asalin jihar Gombe ce kuma an haife ta a shekarar 1961. Ta samu wannan mukami a watan Fabrairun 2017.

3. Justice Maryam Aloma Mukhtar

Justice Maryam Aloma Mukhtar ita ce Mace ta farko da ta zama babbar mai shari’a a Najeriya. An haife ta a 1944 kuma 'yar asalin jihar Kano ce. Ta samu wannan mukami a shekarar 2012.

4. Farfesa Fatima Batoul Mukhtar

ADVERTISEMENT

Farfesa Fatima Batoul Mukhtar ita ce Mace ta farko da ta zama shugabar jami’a a arewacin Najeriya. An haife ta a 1963, 'yar asalin jihar Kano ce. Ta zama shugabar Jami'ar Tarayya da Dutse a 2016.

5. Justice Zainab Bulkachuwa

Justice Zainab Bulkachuwa ce Mace ta farko da ta zama babbar shugabar kotun daukaka kara ta Najeriya. An haife ta a 1950 kuma 'yar asalin jihar Gombe ce. Ta samu wannan mukami a shekarar a 2014.

Banda su, ku bayyana sauran matan arewa da su suka taka rawar gani bisa gudunmawar da suke bada wa wajen raya al'ummar mu.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT