ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Masu garkuwa da mutane sunyi gaba da wani ango da amaryar sa ranar daurin auren su

An saci Yakubu da amarya shi a hanyar su na zuwa inda za’a daura masu aure

An ruwaito cewa Wani Moses Yakubu da amarya sa tare da abokinan shi sun shiga hannun masu garkuwa mutane a hanyar su na zuwa wajen daurin aurensu.

A bisa rahoton da Punch ta fitar ranar lahadi 9 ga watan Satumba yan bindigan sun sace amarya da angon ta a Akunnu Akoko na Jihar Ondo.

Hukumar  yan sanda na jihar sun tabbatar da haka kuma ƙwamishnan yan sanda na jihar Gbenga Adeyanju ya kafa wani tawaga daga cikin jami’an hukumar don kuɓutar dasu daga hannun yan bindigan.

Kakakin hukumar yan sanda na jihar Femi Joseph ya sanar cewa ƙwamishnan ya kafa wani tawagar wanda zata kuɓutar da su daga hannun yan bindigan kuma zata kama wadanda suka saci su.

ADVERTISEMENT

Bisa ga rahoto Yakubu tare da amaryan sa sun taso ne tun daga garin Okene na jihar Kogi zasu Garin Akure na jihar Ondo inda za’a daura masu aure tare da abokanan ango da ƙawayen amarya.

Barayin sun sako amaryan da yar uwan ta amma har yanzu angon da sauran abokanan shi suna hannun su.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT