ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kwana biyu bayan samun damar yin beli, Maryam tayi bikin zagayowar ranar haihuwa (hotuna)

Kalli hotunan bikin murnar ranar haihuwar diyar su Alisha da Maryam wanda ake zargi da laifin kashe mijinta kuma uban diyar

Diyar su da tsohon mijinta marigayi Bilyaminu Bello ta cika shekara daya da haihuwa shine aka  hada mata biki cikin gida dan raya mata ranar.

Hukuncin Kotu kan karar ta

Wannan lamarin ya faru kwanan biyu bayan mai shari'a Yusuf Halilu na kotun tarayya ya bata damar yin beli bisa ga dalilin daukar juna biyu da take.

Kotu ta bata damar ne yayin da aka yi zaman saurara kara ranar laraba 7 ga watan maris bayan rokon da tayi kan barazanar da take fuskanta kan lafiyar jikin ta sakamakon cikin da take dashi wanda ya kai tsawon kusan wata hudu.

ADVERTISEMENT

Alkalin ya nemi kotu da ta bayar da damar beli ga Maryam bisa cikin da take dauke dashi wanda ya kai na tsawon wata uku.

Kasancewa an daure Maryam a gidan kaso kuma daga nan take ziyartar dakin sauraron kara,  alkalin ya nemi kotu da ta ba maryam damar cigaba da halartar kotu kan karar da aka shigar kanta daga gida domin kula da juna biyun da take dauke dashi.

Tsokacin jama'a kan hotunan

Anyi korafe  korafe kan wannan hoton da ya yadu a shafuka da dama na kafafen sada zumunta. Wasu na ganin cewa yin haka bai kamata kasancewa ba da dadewa ba ta fito daga kurkuku.

ADVERTISEMENT

Wasu kuma na ganin cewa wata kila ba ita ta hada bikin ba, yana iya kasancewa yan uwanta ne suka hada don faranta ma diyar rai kamar yadda sauran iyaye keyi ga yaran su idan sun cika shekara bayn haihuwar su.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT