ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Malami wanda yayi sanadiyar cire hannayen yaro zaiyi shekaru 25 a gidan yari

Kamar yadda labari ya bayyana, malamin zai zauna a gidan kaso tsawon shekara ashirin da biyar

Kamar yadda labari ya bayyana, malamin zai zauna a gidan kaso tsawon shekara ashirin da biyar (25).

Idan ba'a manta ba dalibin mai suna, Zubairu Abubakar, ya samu mummanar illar ne sakamakon muzgunawa da malamin yayi masa.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce a kafafen ada zumunta inda jama'a suka yi Allah-wadai da lamarin tare da neman hukuma da gwamnati da su tabbatar sun bi hakkin yaron.

ADVERTISEMENT

Bayan ga korafe-korafe da jama'a sukayi, gwamnatin jihar Gombe ta dauki nauyin kiwon lafiyar yaron. Gwamna Hassan Dankwambo ya bada umarni na a kama malamin cikin gaggawa. Ya kuma sanar cewa zai dauki nauyin karatun sa.

Wannan hukucin da malamin ya samu ya biyi bayan alwashin da gwamnan ya dauka na tabbatar da cewa ya fuskanci hukuncin shari'a bisa ga laifin da aikata.

Kamar yadda ma'abocin kafar sada zumunta ta Twitter ya sanar, wannan mataki ne na kare hakkin yara kana dake fuskantar barazana sanadiyar almajiranci.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT