ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Majalisar datawa ta dage zaman ta domin girmama mututwar daya daga cikin yan majalisa

Majalisar ta daga ranar zaman ta zuwa ranar laraba 21 ga wata kana zata yi juyayin rashin tsohon dan majalisar

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya sanar da hakan a zauren majalisar. Ya kuma bayyana cewa za'a jajanta mashi a zauren a cigaban zaman da zasu yi ranar laraba 21 ga wata.

Sanata Lawan Ahmed yayi kira na a daga zaman domin karrama mutuwar tsohon dan majalisar.

Marigayi dan majalisar dattawa mai wakiltar jihar Bauchi ta tsakiya ya rasu ne a gidan sa dake gwarinpa nan garin Abuja ranar asabar 17 ga wata.

Gabanin mutuwar sa dan majalisar wanda yake wakiltar Bauchi a zauren yana rike da mukamin shugaban kwamitin kwamitin gyaran fuska kan kawo karshen talauci.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT