ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Abubuwa 5 da baku sani ba game da matashi mawakin hausa hip hop

mawakin wadda ya rasu ranar alhamis 14 ga watan Satumba a garin Kano

Hakika masana'antar nishatarwa ta Arewa tayi babban rashi da rasuwar dan matashi mawakin hausa hip hop, amma indai ajalin mutum ya kai babu wanda zai iya kubutar dashi.

Ameer Isa Hassan ya rasu ranar 14 ga watan Satumba a garin Kano sanadiyar hatsarin mota. Anyi jana'izar shi ranar juma'a a layin massalacin juma'a na tarauni.

ga wandada basu san labarin wannan matashin ga abubuwa 5 da ya kamata ku sani;

1. Haifafan Dan jihar kano ne

ADVERTISEMENT

An haifi marigayi Ameer a cikin 2003 a jihar Kano

2. Har zuwa lokacin rasuwar sa mawakin yana koyan darasi a makaranta

Duk da kasancewar shi wanda ya fara shahara a harkar wakoki marigayi bai bari harkar ta dauki hankalin shi wajen koyan darasi. ya kan tafi makarantar boko kuma idan ya tashi yaje na islamiyya. sai karshen mako yake samun damar yin aikin waka. babban burin marigayi shine in ya gama karatu ya zama matukin jirgin sama.

3. Iyayen sa sun mara mai baya

hakika iyayen suka bashi damar fara waka kuma uwar take taimaka masa wajen rubuta wakokin.

ADVERTISEMENT

Ameer ya canza makarantu domin masoyan sa sukan tunkare shi idan yana koyan darasi.

4. Ya fara waka tun yana jjs 1 na makarantar sekandare

matashin ya fara waka ne domin tun yana dan karami yake muradin waka. ya fara waka ne domin ya nuna ma duniya cewa matasa daga yankin arewaci kasar nan na iya rera waka kuma su yi nasara.

5. Yayi wakoki da dama kuma yayi wasa tare da sauran shaharren mawaka

cikin wakokin da marigayi yayi akwai "boss", "champion", "ilimin boko da addinin musulunci", "dance for me" da dai sauran su.

ADVERTISEMENT

Matashin wadda ake wa lakabi "karaminsu babbansu" yayi waka tare da shaharraru da dama kuma yayi wassanni da dama a wurare daban-daban#

Allah ya jikanshi da rahama, Ameen.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT