ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Salah ya lashe kyautar gwarzon shekara ta nahiyar Afrika

Wannan shine karo na farko da dan wasan kasar Masar zai karbi kyautar gwarzon shekara

Mohamed Salah na kasar Egypt ya lashe kyuatar gwarzon shekara ta nahiyar Afrika wanda hukumar CAF ta gudanar a kasar Ghana jiya alhamis 4 ga watan Janairu 2018.

Dan wasan Liverpool ya doke abokin aikin sa na kungiyar Sadio Mane na kasar Senegal da kuma dan wasan Dortmund Pierre Emerick Aubameyang na kasar Gabon wajen karban kyuatar.

Salah ya nuna gwanintr shi bara inda ya taka muhiman rawan gani a kungiyar AS Roma har ga sabon kulob dinsa ta Liverpool wanda har yanzu shine dan wasa mafi kwallaye a kungiyar a kakar bana.

ADVERTISEMENT

Hakazalika dan wasan ya taimaka wajen ganin kasar shi Egypt ta tsallake tsiradi na buga gasar cin kofin duniya wanda za'a gudanar a kasar Rasha bana.

Wannan shine karo na farko da Salah zai amshi kyautar gwarzon shekara ta CAF.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT