ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Jam'iyar PDP bazata kara hawan karagar mulkin kasa

Ministan ya kara da cewa yan Nijeriya na farin ciki da shugabancin shugaba Buhari kuma baza su kara zaben jam'iyar PDP.

Ministan ya kara da cewa yan Nijeriya na farin ciki da shugabancin shugaba Buhari kuma baza su kara zaben jam'iyar PDP.

Wannan labari ya fito jim kadan bayan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda ke jam'iyar PDP yace ba zai samu walwala ba sai mulkin kasar ya koma ga hannun jam'iyar sa.

Lai Muhammed ya fadi haka a jihar Jigawa yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan wata taron da ma'aikatar shi da ma'aikatar wayar da kan jama'a ta hada. Ministan yace shugaba Buhari ya cika mafi yawancin alkawullan da ya dauka yayin da yake kamfe.

Kamar yanda jaridar Vanguard ta fitar, ministan yace gwamnatin shugaba Buhari ta samu nasara wajen tabbatar da tsaro, inganta harkan kasuwanci, bunkasa harkan noma a kasar da dai sauran ire-ire ayyukan cigaba.

ADVERTISEMENT

Sai dai wannan bayanin ya fito kwanan biyu bayan jigon jam'iyar APC Bola Tinubu ya sanar cewa shugaba bai da tabbataciyar tikiti a zaben 2019 karkashin jam'iyar.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT