Pulse.ng logo
Go

Labarin kwallon kafa Ko kun gan sabuwar mota da dan wasan real madrid ya siya

Ga hoton dan ƙwallon da motar kamar yanda ya dora a shafin sa na instagram

  • Published:
Ronaldo tare da sabuwar motar shi play

Ronaldo tare da sabuwar motar shi

24/7 Live - Subscribe to the Pulse Newsletter!

Dan wasan Real madrid Cristiano Ronaldo ya samu karuwa cikin jerin motocin da ya tara masu tsada.

Zakaran yan ƙwallon turai ya dora hoton motar wanda kimanin ta ta kai N162M (£350,000) a shafin shi na instagram.

A cikin hoton Cristiano ya tsaya kusa da motan kuma yaron shi yana gefen kujarar mai tuki.

Ronaldo tare da sabuwar motar shi play

Ronaldo tare da sabuwar motar shi

 

Motar kerar Ferarri (Ferarri F12TDf) ne kuma ya shiga cikin jerin motocin da dan kwallon ke da shi.

Cikin jerin motoci masu tsada da dan wasan Real madrid ya tara akwai Porsche 911 Turbo S, Bently GT Speed, Bentley Continental GTC, Ferrari 599 GTB Fiorano, Rolls Royce Phantom Drophead Coupe, Ferrari F430, Koenigsegg CCX da sauransu.

tare da  daya daga cikin motocin shi play

tare da  daya daga cikin motocin shi

 

Ya siyo sabon motar bayan ya taimaka ma tawagar yan ƙwallon ƙasar Portugal wajen cin nasara a wasan share fage na buga gasar kofin duniya inda suka gama da kasar Hungary da Faroe Island.

Dan wasan zai koma ga tawagar Real madrid amma ba zai buga wasan su da Levante ranar asabar 9 ga watan Satumba sanadiyar dakatarwa da aka bashi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.