Labarin kwallon kafa Fittacen matashi ya samu karbuwa a PSG

Dan wasan ya gabatar da kanshi bainar masoyan kungiyar kuma yayi hira da manema labarai

  • Published:
Mbappe ya samu karbuwa a PSG play

Mbappe ya samu karbuwa a PSG

24/7 Live - Subscribe to the Pulse Newsletter!

Fitaccen matashi dan wasan kasar Faranasa ya samu karbuwa yayin da ya gabatar da kansa a bainar jama’ar sabon kungiyar sa.

Kylian Mbappe ya koma PSG daga Monaco a cinikin bashi wanda ake sa ran komawa na dindindin.

Matashin mai shekara 18 ya gana da manema labarai bayan ya samu karbuwa daga magoya bayan PSG.

tare da shugaban kulob play

tare da shugaban kulob

 

“Ina mai farin  ciki shiga wannan kungiyar wanda take daya daga cikin kungiyoyin na duniya da suka shahara” maganar Mbappe yayin da aka gabatar dashi a filin parc des prince.

Mbappe wanda ya gabatar da kanshi tare da iyalin shi yace zai zage damse wajen taimakon PSG da samun nasara.

Mbappe tare da mahaifin shi da kanin shi play

Mbappe tare da mahaifin shi da kanin shi

 

Ana sa ran cewa dan kwallon zai bayyanar da kanshi a fili ranar juma’a  a wasan Ligue 1 da PSG zata yi da Metz.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.