ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan ƙwallon Monaco na shirin komawa kungiyar PSG

Gidajen radiyo france info da RMC sun sako rehoto cewa ƙungiyar tayi yarda da siyan dan wasan a kan euro miliyan 180

Mbappe na shirin komawa PSG

Matashi dan ƙwallon Monaco Kylian Mbappe zai kaddamar da shirin komawa ƙungiyar PSG idan ya tafi babban birnin ƙasar Faransa ranar litinin bisa ga labarun da ke yaduwa gidajen labarai na ƙasar ranar lahadi.

France info da RMC sun kawo rahoto cewa PSG ta yarda da ta biya euro miliyan 180 don kawo matashin mai shekara 18 ƙungiyar.

Wannan zai sa dan wasan ya kasance dan ƙwallo mafi tsada na biyu a kasuwar siya da siyarwa na yan wasan turai na 2017 bayan Neymar wanda ƙungiyar PSG ta siya a kan euro miliyan 222 daga Barcelona.

Ana kyutata zaton cewa Mbappe wanda zai tafi garin Paris don haduwa da sauran yan wasan kasar France don shirin buga wasa tare da ƙasar Holland da Luxemboug zai yi amfani da damar wajen kaddamar da cinikin komawa PSG.

ADVERTISEMENT

Dan kwallo wanda Real madrid na sa ran siya bai samu damar buga wasan da Monaco ta buga da Marseille a makon da ya gabata kasancewa an aje shi benci.

Matashin wanda ake kwatanta da Thiery Henry koma Monaco yana da shekara 17 kuma ya samu buga wasanni hudu ma ƙasar France.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT