ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kalli tsohon hotunan jaruma tare da mahaifiyar ta da ya birge

Jaruma Maryam Booth tana mai alfahari da mahaifiyar ta kamar yadda hoton su tare ya bayyana.

Ta wallafa tsohon hotunan su tare a shafin ta ma Instagram sanye da alamar soyayya don nuna kaunar da take mata.

Zainab Booth wacce take mahaifiyar Maryam da Ramadan da Amude Booth tana daya daga cikin tsofin jarumai da suka raya masana'antar fina-finan hausa.

Yaran ta sun gaje ta a wannan fanin kuma suna taka rawar gani a masana'antar. Maryam tayi fice a matuka a dandalin fim hakazalika Ramadan Booth da Amude Booth wanda ke hadawa da yin waka.

A cikin shekarar 2017 Ramadan Booth yayi nasarar lashe kyuatar gwarzon shekara na masana'antar fim a gasar da mujallar African Voice ta sirya a birnin London.

ADVERTISEMENT

Ya samu kyautar tare da jaruma Nafisa Abdullahi wanda ta samu kwatancin haka a bangaren mata.

Hirar shi da BBC hausa gabanin samun kyautar, Ramadan ya bayyana cewa dalilin da yasa yan gidan su ke fiitowa a fina-finan hausa shine don kawar da zargin da ake wa yan fim na cewa yan fim na bata tarbiya.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT