ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

'Kada ku yarda da afuwar da jam'iyar PDP ta nema' - sakon jigon APC ga yan Nijeriya

Bola Tinubu,  ya bayyana hakanne a gaggarumin taron lakca da aka shirya don raya bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekara 66 a duniya

Ya kwatanta afuwar da jam’iyyar ke nema a matsayin barawon da ke neman afuwa bayan an kama shi yana aikata satar.

Bola Tinubu,  ya bayyana hakanne a gaggarumin taron lakca da aka shirya don raya bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekara 66 a duniya.

A farkon makon nan ne shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus ya bukaci ‘yan Nijeriya da su yi masu afuwa akan kurakurensu a shekaru 16 da suka yi su mulki a kasar.

Jigon jam'iyar mai mulki yana mai ikirari cewa gafarar da jam'iyar adawa ta nema salon yaudara ne domin samun karbuwa wajen al'ummar kasar.

ADVERTISEMENT

Ya kalubalenci jam'iyar inda ya bayyana cewa ita ta kawo ci baya a kasar sakamakon ayyukan cin hanci da rashawa da ya yadu a zamanin shugabancin ta.

Yace jam'iya ta samu dama na samad da cigaba a kasar amma sai dai ba'a cinma wannan matsaya ba.

Daga karshen tsohon gwamnan ya jaddada cewa jam'iyar APC tana dap da kawo canji kamar yadda ta dauki alkawari yayin neman kuri'a.

Ya kuma yabawa shugabanci shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kokarin da yake wajen kawo gyara duk barazanar da yake fuskanta.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT