ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mataimakin shugaban kasa ya kaddamar da taron tattalin arziki da zuba jari tsakanin jihar Kano da Legas

Manyan yan siyasa da masu ruwa da tsaki a fannoni daban daban sun halarci wannan taron wanda aka gabatar a garin Epe dake nan jihar Legas ciki har da Gwamnonin jihar Legas, Kano da Kebbi tare da attajirin dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote

Taron wanda aka mataimakin shugaban ya kaddamar zai samu halarcin kwararru a fannoni daban daban daga cikin kasar Nijeriya har da yan waje inda zasu bada jawabai kan hanyoyi da zai taimaka wajen bunkasa harkar kasuwanci tsakanin jihohin.

Taron zai gudana ne cikin kwana biyu tsakanin ranar laraba 28 ga watan Febreru zuwa 1 ga watan maris.

A jawabin sa wajen kaddamar da taron Osinbajo ya jinjina ma gwamnonin bisa wannan matakin da suka dauka na hada gwiwa tare da kula kyakyyawar alaka wajen bunkasa harkar kasuwanci.

Mataimakin ya bayyana kara haske game da ayyukan da gwamnatin tarayya take shiryawa domin tallafa ma yan kasuwa masu kananan jari. Yace samad da na'urar dake amfani da hasken rana da zai tallafa wajen samad da hasken wuta a wasu shaguna dake kasuwar sabon gari dake Kano kuma kai ga yanzu ana cigaba da yunkurawa wajen gudanar da shirin a sauran shagunan dake kasuwar.

ADVERTISEMENT

Har illa yau dai mataimakin ya jaddada cewa gwamnatin su zata cigaba da wannan shirin har kasuwanni daban daban dake fadin kasar ciki har da babban kasuwar Ariaria dake kudancin kasar.

Daga karshe Osinbajo ya shaida ma jama'a cewa gwamnatin shugaba Buhari zata cigaba da hada gwiwa da jihohin kasar domin cinma manufofin su.

Taron dai shine na farko da zai faru gamayyar jihohin guda biyu dake kan gaba a harkar kasuwanci.

Manyan baki da suka halarci wannan taron sun hada da Gwamna jihar Legas Akinwunmi Ambode wanda yake shine mai karban baki tare da gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu.

Sarkin kano Mai martaba Alhaji Muhammad Sanusi na biyu da Sarkin Legas Oba Rilwan Akiolu sun hakarci taron hakazalika Alhaji Aliko Dangote da Alhaji Abdulsamad Isiaka rabiu.

ADVERTISEMENT

Sauran bakin da suka ziyarci zauren sun kama da kwamishnonin jihar Legas da Kano, yan majalisar tarayya da na jihohi da manya manyan yan kasuwa dake jihohin har ma da na kasashen waje.

Bayan kammala taron za'a sa hannu ga yarjejeniya wajen aiki da makasudin taron

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

Top 5 female directors in Nollywood

Top 5 female directors in Nollywood

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 reasons Easter was more fun when we were children

5 reasons Easter was more fun when we were children

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT