ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

"Nafika rashin mutunci nida kake kallona bana tsoran kowa sai Allah" Jaruma da wani jigo na Kannywood

Lamarin dai ya jawo cece-kuce tsakanin masoyan ta masu bibiyan shafinta. Wasu sun bada ra'ayi na tayi hakuri kar ta dauki mataki.

Duk da cewa bata bayyana suna wanda take mayar ma raddi, jarumar ta bayyana cewa baza ta damu ba idan har aka kore ta daga Kannywood.

A sakon da ta wallafa a shafin ta na kafar sada zumunta, tauraruwar fim ta bata boye irin rashin mutunci da zata iya yi ga wanda ke neman fushin ta.

Tana mai cewa "Na fika rashin mutunci kuma ni da kake kallo bana tsoron kowa sai Allah".

ADVERTISEMENT

Ga cikakken sakon da ta fitar kamar haka;

"Babu abunda yadameni dakai idan kaga dama kasa a koreni a kannywood dan nasan bakaine me bada daukaka ba allah ne dan haka wallahi nafika rashin mutunci nida kake kallona bana tsoran kowa sai allah ni ummah Shehu nafi karfin nabaka hakuri batare da namaka laifiba dan kasa anyi dcasting dina saime kamanta da allah shine meyi kafin kaima kanka ai ammaka dan haka bacire ni yakamata ayiba korana yakamata kayi nonsense nibazansa hoto ina fadanci ba don babu abunda nake nema agun kowa sai gun Allah kaje katambayi waye ummah shehu za’agayamaka irin rashin mutuncin dazanyi kuma idan katashi tambaya kazo unguwarmu katambaya anan ne zakaji ainihin halin ummah babu wanda ya isah naime fadanci idan ina sonka Ina sonka idan bana sonka bana sonka ni haka nake dan haka to hell with you".

Haka kuma wasu na ganin dai-dai ne idan ta nuna ma wanda ke neman ta da mummunar harka halin ta na rashin mutunci domin kauce ma faruwar haka nan gaba.

Idan ba'a manta ba a kwannan baya, Ummah Shehu, ta jawo tseigumi a kafafen sada zumunta bisa ga tambayoyi da mai gabatar da shiri yayi mata hirar ta da telebijin na Arewa24 a cikin wani shiri na musamman.

ADVERTISEMENT

Hirar ta da BBChausa,  jarumar tana mai cewa ""Ni ban ji haushi ba saboda muna hira ne da Momo akan nishadandartawa ba wai muna hira ne kan addini. duk wanda ya kalli hirar yasan muna wasa ne da dariya a cikin sa".

Ummah Shehu tana mai goyon bayan sauran jarumai mata wajen dogara da kansu a masana'antar fim. Wannan fashin bakin da tayi wata kila na jan hankali domin tabbatar da bakan ta na gogawa da sauran mazajen dandalin fim wajen shiryawa da daukar nauyin shiri.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT