ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Iyalen marigayi sunyi ma shugaban kasa godiya bisa karramawa da yayi

Mohammed Fawehinmi ya kara da yi gwamnati godiya bisa matakin mayar da ranar 12 na watan Yuni a matsayin ranar dimokradiya a kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari a wata sanarwa da aka fitar ranar 5 ga wata shugaba  ya sanar cewa an sauya ranar dimokradiya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni don karrama zaben dimokradiya da aka gudanar cikin shekarar 1993.

Duk a cikin sanarwar shugaban ya bayyana cewa za'a karrama Gani Fawehinmi da matsayin GCON bisa rawar da ya taka wajen tabbatar da tsarin dimokrdaiya da yakin neman yancin yan kasa.

A wata hira da yayi da manema labarai, babban dan dan marigayin, Mohammed Fawehinmi ya isar da godiyar sa ga shugaban bisa matsayin da ya baiwa mahaifin su.

Yana mai cewa"Muna ma gwamnatin tarayya godiya da wannan mutuntawa. Munyi farin ciki kuma mun amince da kyautar.

ADVERTISEMENT

Bayan Fawehinmi, shugaban zai kuma karrama Babagana Kingibe wanda ya tsaya takara tare da Moshood Abiola a matsayin mataimakin sa. Zai samu kyautar GCON.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT