Pulse.ng logo
Go

Itse Sagay Sanatoci na amsar miliyan N29.3 ko wani wata

Shugaban ƙwamitiin masu ba shugaban kasa shawarwari ya bayyana ainihin yawan kudin da ko wani sanata ke amsa duk wata a matsayin albashi

  • Published:
Ibrahim Idris: Itse Sagay condemns Senate's resolution play

Prof Itse Sagay

(The Nation)
24/7 Live - Subscribe to the Pulse Newsletter!

Shugaban ƙwamitin masu ba shugaban ƙasa shawarwari Farfesa Itse Sagay yayi suka game da yawan kudin da yan majalisa ke amsa ko wani wata.

Shugaban ya bayyana cewa ko wani sanata yana amsan miliyan N29.3 ko wani wata kuma biliyan N30.2 a duk shekara.

A rahoto da jaridar Nation ta fitar Sagay ya sanar cewa banda albashin da yan majalisa ke amsa ko wani akwai karin alawus na abubuwa da dama.

Yayi wannan bayani ne yayain da yake jawabi a wani taro da aka gabatar a Legas ranar talata 5 ga watan Satumba.

A jawabin shi Sagay ya zargi shugaban majalisa dattawa da son kai kuma baya taimakawa wajen ganin cewa an magance cin hanci da rashawa kamar yada shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yake yaki akai.

A karshe Sagay yace ƙwamitin da yake shugabanta zata iya bakin kokarin ta wajen gurfanar da manyan ma’aikatan banki da ke taimakon masu satar kudin jama’a.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.