ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Hukumar zabe na kasa ta kafa ranakun gudanar zabe na tsawon shekaru 36

Yace tsarin tsayar da takamammen ranar zabuka yana da fa'ida wajen bunkasa tsarin dimokradiyar kasar Nijeriya zuwa sahun sauran kasashen duniya.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar da hakan ranar laraba 28 ga wata yayin da ya zanta da shugabannin jam'iyun siyasa dake kasar.

Bisa Sanarwar da yayi zabukan zasu kasance cikin watan febreru da Maris na ko wani shekara,

Wannan matakin zai fara ne daga watan Febreru na 2019 zuwa 2055 kamar yadda hukumar ta kayyade.

Shugaban ya kara da cewa kasashe da dama dake amfanin da tsarin dimokradiya sun rungumi irin wannan matakin na fitar da ranakun gudanar da zabe don haka ba abun tseigumi bane mai bukatar cece-kuce.

ADVERTISEMENT

Yace manufar yin haka shine domin tsayyar da takamammen ranar gudanar da zabe kuma zai taimaki hukumar matuka wajen shiryawa kafin ranar zaben.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT