ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yadda hannayen almajirin da malamin sa yayi sanadiyar gutsirewar su ya koma

A makon da ya gabata kotu ta zartar da hukunci game da malamin. Zaiyi shekaru ashirin da biyar a gidan kaso sakamakon laifin da ya aikata.

Kamar yadda hotunan sa yake yawo a kafafen sada zumunta, dalibin ya samu sauki sosai bayan jinyar da yayi a asibiti.

A makon da ya gabata kotu ta zartar da hukunci game da malamin. Zaiyi shekaru ashirin da biyar a gidan kaso sakamakon laifin da ya aikata.

Rawar da gwamnatin Gombe ta taka game da lamarin

Wannan hukucin da malamin ya samu ya biyo bayan alwashin da gwamnan ya dauka na tabbatar da cewa ya fuskanci hukuncin shari'a bisa ga laifin da aikata.

ADVERTISEMENT

Idan ba'a manta ba dalibin mai suna, Zubairu Abubakar, ya samu mummanar illar ne sakamakon muzgunawa da malamin yayi masa.

Wannan lamarin ya janyo cece-kuce a kafafen ada zumunta inda jama'a suka yi Allah-wadai da lamarin tare da neman hukuma da gwamnati da su tabbatar sun bi hakkin yaron.

Bayan ga korafe-korafe da jama'a sukayi, gwamnatin jihar Gombe ta dauki nauyin kiwon lafiyar yaron. Gwamna Hassan Dankwambo ya bada umarni na a kama malamin cikin gaggawa. Ya kuma sanar cewa zai dauki nauyin karatun sa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT