ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Zaman aure ya fiye mun kudin da zan samu da ma komai da komai - inji jaruma

Jarumar tana daya daga cikin yan matan masana'antar Kannywood da zasu ajiye yin fim da zaran sunyi aure domin mayar da hankali wajen kula da iyali

Hannatu Bashir tana daya daga cikin jarumai mata da ake damawa dasu a masana'antar yin fim kuma tayi fice wajen shirya fim da kuma haskawa a cikin wasu da dama.

Jarumar wanda tayi fice a harkar shirya fim tana bada dan karin haske na cewa tana dab da yin aure kuma Allah ya kaddarar da faruwar hakan zata dakatar da harkar fim domin bada muhimmanci wajen kula da iyalin ta.

Hirar ta da wakilin BBC Hannatu tana mai cewa "Ko wace mace tana son ta ganta a gidanta kuma tana kula da iyalen ta. Idan ina da mijin yanzu idan nayi aure, ka gan zan fita da safe zuwa wajen aiki wa zai kula dashi? Idan kuma na fara tara yaya wa zai kula mun dasu?.

ADVERTISEMENT

Ka gan ya zama dole in hakura da daya. Kuma harkar fim dinmu ba a iya kano kadai muke yi muna iya zuwa wasu garuruwa muyi.

Ina da miji zai barni in tafi wani gari inje inyi kwana biyar zuwa goma wajen daukar fim? kaga abu ne mai kamar wuya.

"Ni daia zaman aure ya fiye mun kudin da zan samu kuma ya fiye mun komai da komai ma".

Hannatu wanda ta kwashi sama da shekara bakwai a dandalin nishadantarwa tayi karin haske game da zargin da ake yawan yi ma yan fim na cewa su yan iska ne.

A cewar ta mafi yawanci mata dake aikata hakan bata-gari ne wadanda suke fakewa da cewa su yan fim ne.

ADVERTISEMENT

Tace mafi yawanci katin bogi suke yawo dashi da yin karya cewa su yan fim ne domin idan aka bibiya sau da dama  jaruman basu san da zaman su ba a masana'antar.

Tace irin hakan yana faruwa sosai kuma mafi yawanci ire-iren yan matan da zarar an kama su sai su fake da cewa suna fim tare da nuna katin shaida na karya.

Jarumar wanda ta shirya shirin Sarauniya, Kukan Kurciya da Mairo da dai wasu fina-finai daban tace yin fim sana'a ce kamar sauran sana'o'i kuma yadda ma'aikata ke zuwa masana'antar su haka suma ke zuwa daban farfajiyar su.

Akalla fina-finai hamsin ta fito a ciki cikin tsawon shekara bakwai da tayi a dandalin nishadantarwa ta kannywood.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

Top 5 female directors in Nollywood

Top 5 female directors in Nollywood

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 reasons Easter was more fun when we were children

5 reasons Easter was more fun when we were children

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT