ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnati Buhari na tafiyar da mulki tamkar bata san abun da take yi ba - Inji tsohon gwamna

Ya kara da cewa gwamnatin bata aiwatar da wani aikin azo a gani ba kuma rawar da take takawa tamkar ayyukan yabo ba fallasa.

Malam Ibrahim Shekarau yace gwamnatin Buhari tana gudanar da mulki tamkar bata san abun da take yi ba.

Tsohon gwamna wanda ke neman kujerar shugaban kasa a zaben 2019, yayi wannan bayani ne a hirar da yayi da BBC hausa.

Shekarau wanda a baya yayi gwagwarmayar siyasa tare da goya bayan Shugaba Buhari yana mai cewa "Hatta wadanda suke adawa da gwamnatin sun yi mamakin yadda ta gaza wurin aiwatar da abubuwan da ta yi alkawari".

Tun ba yau ba ake cacar baki tsakani gwamnatin APC wanda ke samna kujerar mulki a halin yanzu da jam'iyar adawa ta PDP wanda ta mulki kasar tsawon shekaru 16.

ADVERTISEMENT

Game da zarge-zarge da PDP take mata, APC tana mai daga kirji cewa ta farfado da tattalin arzikin kasa wanda jam'iyar adawa ta ruguza a tsawon shakarun da tayi a kujerar mulki.

APC ta kara da cewa ta sanya kasar kan hanyar dogaro da kai ba da hanyoyin samun kudaden shiga banda na man fetur.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT