ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

'Gwamnati bata biya kudin fansa ba gabannin sako yan matan Dapchi'

An dawo da matan ne ta hanyar bayan fage kuma har yanzu ana cikin kayyade adadin su, a halin yanzu dai an tsaya kan 101kuma daga cikin su guda 5 sun rasu

Ministan watsa labarai Lai Muhammed ya sanar da haka yayin da ya zanta da manema labarai kafin ya shiga zaman taron majalisar shugaban kasa a Aso villa.

Ministan yace sakin yan matan da boko haram suka yi ya faru ne sakamakon kyakyawar yarjejeniya da aka da mayakan a bayan fage.

A wata sanarwa da ya fitar, ministan yace har yanzu ana kokarin kayyade adadin yan yan matan da suka dawo.

A halin yanzy dai an tsaya a kan 104 kamar yadda fadar shugaban kasa ta sanar a shafin ta na twitter.

ADVERTISEMENT

A cewar ministan"Domin ceto yan matan, gwamnati ta gano cewa rikici da tashin hankali tsakani gwamnati da mayakan ba mataki da ya kamata bane, domin yin haka zai yi ma rayuwar yaran barazana, don haka muka dauki matakin sasanta mayakan.

Lai Muhammed ya kuma bayyana cewa a lokacin da mayakan ke kokarin mayar da yan mata sai da aka dakatar da ayyuka a garin domin ganin an mayar dasu lamin lafiya ba tare da wata tarzoma ko lahani.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT