ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ya zama dole inyi iya bakin kokari na wajen mayar da taskar mulkin kasa zuwa jam'iyar PDP a zaben 2019

Yace hakkin shi wajen mayar da jam'iyar inda take a da domin ta sanadiyar shi ta samu rashin nasara

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya sanar da aniyar sa na mayar da taskar mulkin kasar zuwa jam'iyyar PDP a zaben 2019.

A bisa labarin da jaridar Vanguard ta fitar Jonathan ya alhakin reshin nasara da jam'iyar ta samu a zaben 2015 ga kansa.

Yace ya zama hakkin shi wajen mayar da jam'iyar inda take a da.

Tsohon shugaban kasan ya fadi haka yayin da amshi ziyarar Bode George yayin da jigon jam'iyar PDP ya kawo masa ziyara a gidan sa dake nan jihar Bayelsa.

ADVERTISEMENT

Bode George daya daga cikin yan takarar kujerar shugaban jam'iya ne kuma jigo ne a jam'iyar.

Jonathan ya shawarci jam'iyar da ta tabbatar ta samu goyon bayan yan Nijeriya kana ya kara da cewa kuskuren da ya faru baya ba zai sake faruwa ba.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT